An tura ƙarin jami’an tsaro garin Ƙaya a ƙaramar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna bayan wasu bayan wasu hare-hare masu nasaba da ramuwar gayya da suka auku tsakanin ‘yan sintiri da wasu da ake zargin ‘yan fashin daji ne.
Al’amarin ya yi sanadin halaka kusan mutum ashirin, da raunata wasu da dama, da kuma lalata dukiya mai ɗumbin yawa.
Kwamishinan tsaro a jihar, Samuel Aruwan ya faɗa wa BBC cewa jami’an tsaro sun duƙufa domin gano waɗanda suke da hannu a ta’annatin.
Game da binciken ƴan bindigar, kwamishinan ya ce “ana nan ana ta bin sawunsu, idan aka yi la’akari da wannan yankin yana kusanci da ƙananan hukumomin Ɗandume da Sabuwa a jihar Katsina”
Ya nuna rashin jin daɗi game da yadda ake farwa wasu mutane da ake zargin ƴan bindiga ne lamarin da ya ce yana “mayar da hannun agogo baya”.
A cewarsa, “akwai makiyaya kusan huɗu da aka far musu aka kuma kashe su, yana da kyau ɓangarori daban-daban a riƙa bin doka da oda, a bar wa jami’an tsaro da gwamnati dama su yi abin da ya kamata su yi a ƙarƙashin doka”.
Yadda lamarin ya faru
Wani mazaunin yankin da ya nemi a ɓoye sunansa, ya tabbatar cewa an girke sojoji a garin domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.
Sai dai ya ce har yanzu, mutane na ci gaba da juyayin lamarin tare da fargabar sake afkuwar haka a gaba.
Game da irin asarar da hare-haren suka haddasa kuwa, bawan Allahn ya ce “da wuya a iya tantance irin asarar dukiyar da aka yi saboda akwai motoci guda kusan shida da aka ƙone, akwai wata mota da wucewa za ta yi ɗauke da kayan amarya ita ma ƴan ta’adda sun cinna mata wuta ta ƙone”.
A cewar mutumin, an ƙone wasu shaguna kusan sama da guda 20 da su ma aka cinna musu wuta kuma suka ƙone ƙurmus.
Ya ce ƴan bindigar sun isa garin ne a kan babura 50 zuwa sama kuma kowane babur yana ɗauke da mutum uku-uku, “ƙila ana iya cewa sun kai 150 abin da ya yi sama.”
Ya bayyana cewa da alamu ƴn bindigar sun yi bazata ne saboda “shirin da aka yi ta yi na ƙoƙarin a shirya musu ba a riga an shirya musu ba, kuma yanayin yadda suka zo da manya-manyan makamai, ba kowa ne zai iya tunkarar su ba”.
Sai dai ya ce daga baya sojoji sun kai musu ɗauki.
Hare-haren ‘yan fashin daji da satar mutane don neman kuɗin fansa, manyan matsalolin tsaro ne da ke ci gaba da addabar garuruwan arewa maso yammacin Nijeriya.