Akalla mutane biyar ne rahotanni suka ce an kashe tare da kona gidaje a wata arangama da aka yi tsakanin ‘yan kasuwa da masu tuka mashinan haya wayo okada a unguwar Dei Dei da ke yankin Abuja Municipal (AMAC) a babban birnin tarayya Abuja.
Wani mazaunin garin ya shaida wa jaridar cewa, hatsarin wani mai babur ne ya jawo tabarbarewar doka da oda a cikin al’umma.
“Mutane biyar da na sani an kashe su a wannan lamarin. Mun yi ta kiraye-kirayen ga jami’an tsaro nomin kawo dauki,” inji mazaunin garin wanda ya nemi a sakaya sunansa.
“Mun shiga cikin matukar damuwa cewa wannan rikicin yana karkata zuwa ga kabilanci.”
Jaridar Daily Trust ba za ta iya tantance adadin mutanen da suka mutu ba, amma daya daga cikin wadanda abin ya shafa ya tabbatar da cewa an kona gidansa.
An kuma ruwaito ce ’yan kasuwar sun kai wa Dan Okadan hari,, wanda suka zarga da yin sakaci da ya kai ga mutuwar fasinjan.
Rahotanni sun ce abokan aikin mahaya okada sun yi yunkurin kubutar da shi daga hannun mutanen dasuka farmaki shi, kuma lamarin ya ci tura daga baya.
Wani labarin kuma ya nuna cewa an kai wa direban tirelar da ya murkushe fasinjan har lahira, inda wasu suka yi ta kokarin kare shi.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, jami’an tsaro sun tashi zuwa wurin domin hana cigaba da afkuwar tashin hankalin
Comments 1