Mahaifiyar ‘ya’ya hudu mai suna Mrs. Glory Ogbewi da danta dan shekara biyu sun kwanta dama a Ime-obi da ke karamar hukumar Ika ta Kudu a jihar Delta.
A cewar jaridar Ika Weekly, wata kafar yada labarai ta yankin Agbor, marigayiyar tana fere rogo ne domin ta soya a tsakanin karfe 2 na rana zuwa 3 na rana lokacin da maharan suka kai mata hari a ranar Alhamis, 4 ga watan Nuwamba, 2021.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa tana dauke da yaronta na karshe mai kimanin shekara biyu a duniya, sai maharan suka yi mata dirar mikiya, inda ta fadi, yaron da ke bayanta ya buge kansa da wani abu mai kauri ya mutu.
A cewar majiyoyin, mai yiwuwa marigayiya Misis Ogbewi ta san wadanda suka kai mata harin don haka; sun tabbatar ta mutu kafin su tafi don hana ta tona musu asiri.
Makwabta sun yi mamakin abin da marigayiyar ta yi wa wadanda suka kashe ta.
Wasu mazauna yankin da suka zanta da Majiyar Jaridar Dimokuradiyya, sun yi Allah wadai da lamarin, inda suka bayyana shi a matsayin na dabbanci, sun kuma yi addu’ar Allah ya Tona asirin masu hannu a cikin lamarin.
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, mijin matar dan asalin garin Aliren, a yankin Alisimie, wanda dillalin magunguna ne ya kasa yiwa manema labarai bayani.
Har yanzu dai rundunar ‘yan sandan jihar Delta ba ta mayar da martani a hukumance kan lamarin ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.