By Ishaq Dabai
Karshen hanyar ne ga wasu ‘yan fashi da ke addabar al’ummomi a karamar hukumar Koton Karfe ta jihar Kogi, kamar yadda jami’an’ yan banga na jihar suka kashe 11 daga cikinsu, a karshen mako, An kama karin wasu da ake zargi yayin da wadanda aka yi garkuwa da su kwanaki biyar da suka gabata
Abin mamaki daya daga cikin wadanda aka kama shine ma’aikacin Hukumar Tsaro ta farin kaya na Najeriya, Sufeto Abdullahi Saidu, An zarge shi da bayar da makamai da bayanai ga masu laifin, tare da wani abokin aikin sa farar hula.inda Kama wadanda ake zargin kamar yadda aka tattara, ya biyo bayan rahoton leken asiri.
Majiyoyi sun fadawa manema labarai cewa ”Alaidi shine shugaban su.Inda Aka kashe shi yayin harin a sansanin su na farko. An kuma murkushe Rabo da wasu karin mutane bakwai.sannan an kashe Madei da wani a sansanin masu garkuwa da mutane na biyu yayin da Umar ya tsere da raunin harbin bindiga amma an sake kama shi. ”
Wadanda ake zargin an kama su suna hannun hukumar tsaro ta farin kaya DSS
Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Muhammed Onogwu, ya ce wannan abin da aka yi ya tabbatar da cewa tsare tsareb tsaro na jihar Kogi yana da karfin da zai iya kawar da duk wasu munanan laifuka.
Ya bayyana cewa ‘yan banga na jihar Kogi sun sami nasarori da yawa a cikin Kogi, matakin da ya danganta da goyon bayan da gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya ba su, da haɗin kai daga’ yan ƙasa da haɗin gwiwa tare da hukumomin tsaro.ya kara da cewa”Gwamnatoci a dukkan matakai za su ci gaba da yin kokari don ci gaba da himma don samar da zaman lafiya a jihar Kogi ta hanyar sanya kowane lungu da sako na jihar cikin hadari ga masu aikata laifuka da masu daukar nauyinsu”.