Wata kungiyar samar da zaman lafiya dake Najeriya WANEP ta ce, a watan Agustan da ya gabata, Yan Najeriya 693 aka kashe a hare-hare daban daban, cikin su harda 183 da suka mutu sakamakon arangamar da akayi tsakanin jami’an tsaro da kungiyoyin yan bindiga dake kasar nan.
Kungiyar ta bayyana dalilan kashe kashen da suka hada da hare haren yan bindiga, tashin hankali, rikicin yan kungiyar asiri, kisan kai, da kisan gilla, da rikici tsakanin makiyaya da manoma, da kuma rikicin dake da nasaba da banbancin jinsi.
Rahotan kungiyar ya kuma bayyana hare hare 66 dake da nasaba da garkuwa da mutane a jihohi 18, yayin da tace, a wata Agustan an sace mutane 496, cikin su harda mata 37, da yara 22.
Kungiyar da ake kira WANEP ta bayyana Jihar Filato a matsayin inda aka fi samun kashe kashe a watan Agusta da ya gabata, da ya kai mutane 122, sai Zamfara mai mutane 121, Kaduna mai 111, sannan Katsina mai mutane 64.
Sanarwar kungiyar ya bayyana cewar an kashe mutane 37 a jihar Neja, 27 a jihar Borno, 26 a jihar Imo, 24 a jihar Rivers, 21 a jihar Ogun sai kuma 18 a jihar Benue.
KARANTA WANNAN LABARIN: Faransa ta gargadi Mali kan dauko Sojojin Haya daga Rasha
Sauran sun hada da 15 a jihar Delta, 14 a Osun, 13 a Lagos, kana 7 a jihohin Ondo da Taraba.
A wani laabrin Kuma na daban
Rundunar yan sandan Nigeria za ta dauki Sabin jami’ai guda 60,000, a cikin shekaru shida masu zuwa.
Babban sufeton yan sandan Nigeria IGP Usman Baba ne ya bayyana hakan, a yau Laraba yayin ziyarar aiki da ya kai ga rundunar yan sandan jihar Kwara a Ilorin, babban birnin jihar.
Wannan shi ne daidai lokacin da shugaban yan sandan ya bayyana Kwara a matsayin jiha mafi zaman lafiya a fadin kasar nan, idan aka kwatanta da sauran jihoh dake Nigeria.
Kazalika sifecton ya ce, rundunar yan sandan za ta dauki sabbin jami’ai akalla 10,000 a kowace shekara, har na tsawon shekaru shida.
“Shugaba Muhammadu Buhari ya ba mu izini mu dauki jami’an‘ yan sanda 10,000 a kowace shekara, har na tsawon shekaru shida masu zuwa nan gaba. Kuma Mun fara amma ba mu yi ba a shekarar 2020. Don haka, za mu dauki na shekarar 2020 da 2021 tsakanin yanzu zuwa nan dan karshen shekara nan. Inda za su sami horo na tsawan watanni shida. Don haka Muna saran nan da zuwa karshen shekarar 2021, za mu Sami Karin jami’ai 20,000 a cikin rundunar Yan sanda ”inji Baba.
Ya kara da cewa za a dauki sabbin jami’an ne daga kananan hukumomi 774 dake fadin kasar nan, inda ya kara da cewa, bayan kammala horas da su, a na duba yuwuwar tura jami’an zuwa jihohin su na asali domin bada gudun mawa wajan wanzar da zaman lafiya a Nigeria.
Tun da farko, a nasa jawabin, Kwamishinan yan sandan jihar Kwara, Mr Tuesday Assayomo ya ce, rundunar yan sandan jihar, ta na fama da karancin jami’ai, inda take da jami’an yan sanda Maza guda 3,500 kacal.