A kalla ‘yan binda da barayin dabbobi 70 ne suka rasa rayukansu a yayin da jami’an soji suka kaddamar da wani sumame a Kachia dake karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.
Sannan Sojojin sun yi nasarar cafke biyu daga ciki masu yiwa ‘yan bindigar safarar kayan aiki a kauyen Kankomi.
Rundunar sojin ta kaddamar da shirin ne domin yaki da kuma kauda ‘yan ta’adda da suka samu da jihar ta Kaduna da muggan laifuka.
Hakan yana fitowa a wani jawabi da shugaban yada labarai na hukumar sojin Manjo Janar John Enenche ya bayyanawa manema labarai da cewa sun yi wa shirin lakabi da suna ‘THINDER STRIKE’, kuma an kirkire shi domin kawo karshen ta’addanci a jihar ta Kaduna.
https://dimokuradiyya.com.ng/yan-bindiga-sun-kakkabo-jirgin-yan-sanda-a-kaduna/
Ya kara da cewa “mun samu bayanan sirri na inda maboyarsu take nan take muka aika ta jirgin yaki, wanda ya koro su daga maboyar tasu, bayan sun tabbatar mana da an kashe 70 daga cikinsu wasu kuma sun gudu tare da raunuka a tare da su”. Cewar Enenche.
“Sannan muna kira ga jama’ar wannan yanki da su bada rahoton duk wani wanda suka gani da rauni domin an dauki matakin da ya kamata a kan lokaci”.
An yabawa rundunar sojin bisa wannan nasara da suka yi na kashe ‘yan ta’adda har 70 a wannan karon, kuma na bukaci mutane da su ci gaba da bawa Jami’an sojin hadin kai wajen bada bayanai da zasu taimaka don ganin an kawo karshen ta’addanci a Kaduna dama Najeriya baki daya.