Gwamnan Kogi Yahaya Bello ya yi fatawar kin yarda da rigakafin korona, inda ya ce an kirkiri rigakafin ne kawai domin a kashe mutane da shi.
Gwamnatin Nijeriya ta ce tana dakon jiran isowar rigakafin guda dubu dari zuwa karshen watan Janairu na kamfanin Pfizer da BioNTech da aka amince a yi amfani da shi.
A wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, Yahaya Bello ya yi tir da rigakafin korona. Inda ya ce ana son kashe mutane ne da shi. Da yake magana ga jama’a, gwamnan Kogi ya ce yana da shakku da rigakafin na Korona, inda ya ce; me yasa har yanzu ba a samar da maganin cutar kanjamau (HIV) ba da sauran wadansu cututtuka da suka addabi al’umma? Ya tambaya.
Sai dai gwamnan bai bayyana wata kwakkwaran hujja da zargin na shi ba dangane da rigakafin korona din da ya ce zai iya haifar da wata matsala ga lafiyar jiki.
Bello ya kara da cewa; “kasa da shekara daya an samar da rigakafin cutar korona. Amma har yanzu babu maganin cutar kanjamau (HIV), Maleriya, cutar daji (cancer), ciwon kai da sauran cutuka da suke kashe mu. Kawai suna son su yi amfani da rigakafin korona su bullo mana da wadansu cutukan da za su kashe mu da shi. Ba zamu yar da ba”. Ya tabbatar.
Gwamna Kogi ya ce akwai bukatar a yi waiwayen abin da ya faru na yarda maganin kamfanin Pfizer ya gurguntar da mutane a Kano. Wanda ya ce wannan kawai ya isa darasi.