Sanata Shehu Sani ya koka da gazawar gwamnati mai ci wajen tunkarar kalubalen tsaro a fadin kasar nan.
Tsohon dan Sanatan wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar wakilai ta 8, a wani sako da ya wallafa a shafin sa na Facebook da aka tabbatar a lokacin da yake mayar da martani game da kashe mutane kusan 42 da aka yi a jihar Sokoto ya ce, lamarin da zai tayar da hankali idan da ace a lokacin gwamnatin da ta gabata ce ya faru. .
A cewarsa wadanda ke da Gum game da kashe-kashen,ba su da bambanci da maharan.
Sanarwar ta ce, “An kashe mutum arba’in ta hanyar konasu kurmus a Sokoto. Wannan ta’asa ce da ka iya haifar da tashin-tashina da kuma yin Allah wadai da gazawar Gwamnati, da a ce ya faru a gwamnatin da ta gabata ne.
“Wadanda suka yi shiru daidai suke da wadanda ba ruwansu da shi; wadanda ba ruwansu da lamarin, daidai suke da wadanda suka aikata wannan mummunan aiki.” Inji Sanata Shehu Sani.
“Babu wani wuri a Duniya da rayuwar ɗan adam ta kasance mai arha, wanda za’a iya kashewa da kuma zubar da shi”.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a jiya Talata wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun yi wa wasu matafiya kwanton bauna kan hanyar da ta hada karamar hukumar Sabon Birni da kauyen Gidan Bawa a jihar, inda suka kona su da ransu kurmus.
Comments 1