Gwamnatin Jahar Kwara ta dakatar da wani shugaban Makarantar Larabci a Ilori, Babban birnin Jahar, sabudda hukunci da ya yiwa ɗalibai mai tsanani sabudda wani laifi da suka aikata a makarantar.
Idan dai za’a tuna akwai wani bidiyo da yayi yawo a ƙarshen hutun mako, wanda ya nuna wasu ɗalibai maza guda 4 na Makarantar Larabci ana dukansu, a yayinda aka tilasta masu zama da ƙafafunsu, a dalilin zargin su da ake sun sha giya.
Acewar sanarwar da Kwamishinar Ilmi ta Jahar Hajiya Sa’adatu Modibbo Kawu, tawagar gwamnati ta ziyarci makarantar da akayi zargin ɗalibai sun aikata laifin shan giya, wanda aka nuno su a bidiyo ana yi masu hukunci, ya saɓawa dokokin makarantar.
KARANTA WANNAN LABARIN:Wata Mota ta Murkushe wasu Yan Makaranta 3 a Osun
Tawagar gwamnati ta ƙunshi Mrs Kawu, Mai taimakawa Gwamna na musamma akan addinin musulunci Alhaji Ɗan Maigoro da Dr Saudat AbduƁaqi na jami’ar Ilorin, da Mallam Lawal Oluhungbebe na Jami’ar Jaha ta Kwara, da Sakataren ƴan jarida na Gwamna Rafiu Ajakaye.
An kuma haɗa tafiyar da DPO Oko Nkama, da wakilin Hukumar jami’an tsaro na Sibil difens, da DSC Parati AbdulHameed
Sanarwar ta kuma ƙara dacewa, Tawagar gwamnati ta kuma saurari Hukumomin Makarantar, da uban yarinya da wasu ɗalibai huɗu da hukuncin ya rutsa dasu.
“Bayan binciken da tawagar gwamnati tayi ta kuma kama shugaban Makarantar da laifin hukuncin, inda gwamnati ta bada umarnin kafa kwamiti da zai duba lamarin, a yayinda aka umarci shugaban Makarantar ya sauka daga mukamin sa, har sai an kammala bincike
Gwamnati ta kuma bada umarnin kai ɗaliban Asibitin Gwamnati domin duba lafiyar su da basu magani