Gwamnati Amurka ta bukaci wasu ‘yan Nijeriya sama da 370 da su fice su bar mata kasa saboda aikata wasu laifuffuka da suka hada da karya dokar shigi da fice da laifuffukan da ke da nasaba da yanar gizo.
Rahotanni sun ce wadannan ‘yan Najeriya an tabbatar da laifuffukan akan su ne a kotunan da ke Jihohin Texas da New York da California da kuma wasu karin Jihohin kasar daga watan Janairu zuwa Yunin wannan shekara.
Jaridar Premium Times da ake wallafawa a Najeriya ta ce alkaluman hukumomin Amurka sun bayyana cewar ‘yan Najeriya sama da 3,000 aka kora da kasar bayan kotuna sun same su da laifi a cikin shekaru 15 da suka gabata, yayin da a cikin watanni 6 na wannan shekara kawai aka samu ‘yan Najeriya 335 da suka shiga Amurka ta hanyar da bata kamata ba, ko kuma suka ci gaba da zama a kasar bayan karewar bizar su ko kuma suka shiga da takardu na bogi.
Su dai wadannan mutane 376 da za’a kora na daga cikin ‘yan Najeriya 901 da yanzu haka ake tsare da su a wurare daban daban da ke kasar ta Amurka.
‘Yan Najeriya na daga cikin baki da ke zama a Amurka da suka fi ilimi kuma suke bada gagarumar gudumawa wajen cigaban Amurka.
Wadannan sun hada da likitoci da injiniyoyi da masana kimiya da kuma malaman jami’oi.