An Kubutar Da Mutane 69 Da Aka Sace a Bauchi
Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar Bauchi, Alhaji Abdulrazaq Nuhu Zaki, ya ce jami’an tsaro da ‘yan banga sun kubutar da mutane 69 da aka yi garkuwa da su a lokacin da suka kai farmaki kan wani sansanin ‘yan bindiga a dajin.
Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a Bauchi yayin da yake amsa tambayi daga ‘yan jarida kan kutsawar ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a kananan hukumomin Toro, Alkaleri, Tafawa Balewa, da Ningi na jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN,: Ta’addanci: Gwamnatin Zamfara ta kafa cibiyar Kula da kiran gaggawa
A cewarsa, “Gwamna Bala Mohammed ne ya jagoranci yakin da kansa. Ya ziyarci yankunan da lamarin ya shafa, ya jajanta wa jama’a tare da karfafa musu gwiwa da su bijirewa masu garkuwa da mutane. Hakazalika ya kara wa shugaban karamar hukumar, ’yan banga, sarakunan gargajiya, jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki kwarin gwiwa.
“Mun haɗu tare sa jami’an tsaro, da ‘yan banga. Mun kutsa cikin dajin ba tare da tsoro ba, muka fuskanci ‘yan fashin. Sai suka gudu amma mutanenmu suka ci gaba da zuwa wajensu.
“Shugabannin mu sun kawo mana rahoton cewa adadin mutanen da barayin suka yi garkuwa da su sun kai 69 kuma an kubutar da su, wadanda suka yi garkuwa da su sun ajiye da yawa daga cikinsu a Bauchi. Mun sake su kuma muka bar su su koma gida.
Kwamishinan wanda ya yabawa ‘yan banga, hukumomin tsaro da kuma al’ummar da abin ya shafa, ya ce korar ‘yan bindigar zai kawo sauki ga mutanen da aka firgita.
“Kwanan nan, muna da baki da suka zo jihar da rakuma da shanu. Suna cikin dajin Lame Burra. Gwamnati ta aike da jami’an tsaro da jami’ai domin samun bayanai daga wurinsu kan aikinsu a jihar. Idan mutanen kirki ne, za a bar su su zauna. Amma idan miyagu ne ko masu laifi, za mu kore su,” ya kara da cewa.