- Majalisar dokokin Oyo ta dakatar da karin wani shugaban karamar hukumar a jihar.
- Da dakatar da shugaban karamar hukumar ya biyo bayan wasu zarge-zarge da ake yi masa.
- Ko a watan Mayun daya gabata majalisar dokokin ta dakatar da shugaban karamar hukumar Irepo, Adediran bisa zargin karkatar da kudade.
Majalisar dokokin Oyo ta sake dakatar da karin wani shugaban karamar hukumar a jihar.
Shugaban karamar hukumar Saki ta yamma, Sarafadeen Omirinde an dakatar dashi a ranar Talata.
KARANTA WANNAN: APC Yanzu Za Ta Iya Gyara Laifukan Data Aikata A Baya – Wike
Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa wannan ba shi ne karon farko da majalisar dokokin ta dakatar da shugaban karamar hukuma ba.
Majalisar ta dakatar da shugaban karamar hukumar Irepo, Mista Lateef Sulaimon Adediran a watan Mayun wannan shekara bisa zargin karkatar da kudade.
Majalisar a ranar Talata ta sanar da dakatar da Omirinde sakamakon wasu zarge-zarge da ake yi masa.
‘Yan majalisar sun sanar da dakatarwar ne domin baiwa majalisar damar gudanar da cikakken bincike kan zarge-zargen da ake yi wa shugaban a wata wasika da suka aike wa majalisar.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa sakataren majalisar ne ya karanta wasikun mai dauke da rattaba hannun kashi biyu bisa uku na ‘yan majalisar dokokin.
Wasu daga cikin zarge-zargen da ake yi wa shugaban da ke cikin rudani sun hada da rashin da’a, rashin bin addini, cin amanar jam’iyya da karkatar da tallafin karamar hukuma ba bisa ka’ida ba.
Daga nan ne majalisar ta umurci mataimakin shugaban karamar hukumar, Mista Gbenga Akinola da ya karbi ragamar mulki daga hannun shugaban.
Shugaban ‘yan majalisa a karamar hukumar shi ne zai karbi mukamin mataimakin shugaba.
A wani labarin kuma, Martanin APC Kan Rusau Din Abba Gida Gida
Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta zargi jamiyyar NNPP, da gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf da aiwatar da ayyukan don zuciya, ta hanyar fakewa da rushe gine ginen jama’a.
Mataimakin shugaban jam’iyyar na Kano Hon Shehu Maigari ne ya yi Allah wadai da aikin jam’iyyar ta NNPP, a yan kwanaki da kama mulkin jihar.