Gwamnatin tarayya ta ce za ta kammala jigilar dawo da ‘yan ƙasar nan da suka maƙale a ƙasashen ƙetare a ranar Asabar mai zuwa 22 ga watan Agustan da muke ciki sakamakon annobar Korona.
Shugaban kwamitin yaƙi da cutar Korona na gwamnatin tarayya Boss Mustapha ne ya bayyana hakan, lokacin da yake ƙarin bayani game da rahoton cutar ga kwamitin a birnin tarayya Abuja.
Boss Mustapha wanda kuma shi ne sakataren gwamnatin tarayya, ya ce ganin cewa a yanzu ana dab da kammala jigilar yan kasar nan da suka rage a kasashen waje, ya sanya gwamnatin tarayya ta amince da sauran filayen jiragen kasar nan su fara shirin ci gaba da ayyukan su.
Har wa yau, Boss Mustapha ya ce, akwai ƙasashe irin su Amurka da haɗaɗɗiyar daular larabawa wato Dubai da kuma Masar waɗanda suka shirya domin dawo da ‘yan asalin ƙasarasar nan da suka aikata laifuka a can kuma suka yafe musu.
Da yake nasa jawabin ministan lafiya Osagie Ehanire ya ce, a yanzu haka ana samun raguwar masu kamuwa da cutar ta COVID19 a kwanakin nan, yana mai cewa hakan ba zai sanya su rage ɗaukan matakan kariya daga cutar ba.
Osagie ya ƙara da cewa a yanzu gwamnatin tarayya ta mayar da hankali ne kan yadda za a rage yawan masu mutuwa sandiyyar cutar a kasar nan.