Gamayyar jami’an JBPT masu sanya ido ta atisayen OSR sun yi nasarar cafke wadansu kayayyaki da kudinsu ya kai naira biliyan 12.5 ya zuwa ranar 5 ga watan Janairu.
Kakakin hukumar Kwastan, NCS, Joseph Attah, shi ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja a ranar Alhamis.
Joseph Attah, ya ce kayayyakin da aka kwace sun hada shinkafar kasar waje da nauyinta ya kai kilogiram 159,506.7-(50kg) da buhun taki na NPK guda 10,447 wanda ake amfani da shi wajen hada abubuwa masun fashewa.
Sai kuma motoci guda 1,974 da Babura guda 895. Ya kara da cewa; sun cafke jarkoki guda 18,690 na mai da wadansu kayayyakin daban.