Rahotanni daga jihar Katsina sun ce an kwantar da mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Faruk Umar Faruk a babban asibitin gwamnati dake garin Katsina.
Jaridar ta Daily Nigerian da ta wallafa labarin, ta ce alamun rashin lafiyar dake damun Sarkin a lokacin da aka garzaya da shi asibiti sun yi kama da na cutar Korona, sai dai wata majiyar tace hawan jini ke damunsa.
A ranar litinin da ta gabata, Gwamnan Katsina Aminu Bello Masari ya bada umarnin rufe fadar Sarkin na Daura, matakin da ya ce ya dauka domin dakile yaduwar annobar ta Korona.
Zuwa wannan lokaci dai jumillar masu dauke da cutar Korona a Katsina ya kai 75, guda 6 sun warke, yayin da annobar ta kashe mutane 5.