Wani bidiyon TikTok ya bayyana yadda wata matashiyar budurwa ta tasa wani namiji mai aure a filin rawa wanda yayi kama da gidan biki tana kada masa kwankwaso, Legit.ng ta ruwaito.
A bidiyon wanda aka wallafa a Monday, 7 ga watan Nuwamba, an ga inda wani mutum ya nuna rashin damuwarsa akan wata dirarriyar budurwa.
@kiki_gh4 ce ta wallafa bidiyon. Abinda yafi daukar hankali shi ne yadda matar mutumin ke wurin a lokacin da budurwar ta tasa shi gaba tana rawar mai daukar hankali.
Ta durkusa kasa ne inda take kada masa kwankwaso ta wani yanayi mai matukar daukar hankali.
Ganin za ayi babu ita, matarsa ta yi gaggawar zabura inda ta shiga filin ta janye mijinta. Bidiyon ya dauki hankalin mutane da dama wanda fiye da mutane 1000 sun nuna alamar jinjina karkashin bidiyon.
KU KARANTA: Yadda budurwa ta baro Dubai don taje auren aminiyarta, ta riski ashe saurayinta ne angon
Wata ‘yar Najeriya cike da takaici da alhini a dandalin TikTok inda ta bayyana yadda babbar kawarta ta kwace mata saurayin da take matukar kauna, Legit.ng ta ruwaito.
Budurwar mai suna Princess Toria ta bayyan a wani gajeren bidiyo wanda ta wallafa ranar Juma’a, 4 ga watan Nuwamba inda tace kawarta ta yi mata wuff da saurayi.
A cewar Princess, ta dawo Najeriya ne don ta bai wa aminiyarta mamaki hakan yasa bata sanar da ita batun zuwanta ba, ashe zata tarar da labari mai firgitarwa.
Kamar yadda tace, kawarta za ta yi aure don ana shirin da rana, hakan yasa taga dacewar taje tayi mata kara.