An kwashi ‘yan kallo yayin da wani dan Najeriya ya lallaba zuwa banki da cikakken shirinsa din jiran amsar kudi, Legit.ng ta ruwaito.
Matashi ya bayyana a bankin da katifa, murhun gas da tukunya don yin aikace-aikacensa na gida kafin ya amshi kudinsa daga banki.
KU KARANTA: An kuma: Wani mutum ya faɗi matacce wurin jiran cirar kuɗi a banki
Nan da nan kwastomomi suka sha mamaki inda suka nuna goyon baya a gare shi inda suka ba shi masauki tare da jera masa kayan yadda ya dace.
Mutane da dama sun nuna rashin jindadinsa dangane da yadda bankuna suke tafiyar da lamurransu a kan kudade.
Matashin dan Najeriya ya bayyana a bankin inda ya ba mutane da dama mamaki rike da marhunsa na has, gado da tukunya.
Kamar yadda ya ce, yana da kudade da dama a asusunsa amma ya rasa yadda zai yi amfani da kudin don tafiyar da lamurransa na rayuwa.
Ya shiga jeri inda ya bukaci banki ya bude masa sannan ya nemi lallai sai sun ba shi kudadensa. Nan da nan jama’a suka nuna goyon bayansu kan wannan matakin da ya dauka.
CNG Ta Nemi CBN Ya Sauya Manufofin Musanya Kuɗi, Da Kayyade Fitar Da Kuɗin
Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya, CNG, ta jaddada bukatar ta na gaggauta sauya tsarin takaita fitar da kudade na Babban Bankin Kasa (CBN) da kuma lokacin da za a yi musanyar tsofaffin takardun kudin Naira.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa A wata sanarwa da mai magana da yawun CNG, Abdul-Azeez Suleiman ya fitar, ya ce ‘yan Najeriya ba za su iya lamuntar ” rashin kudi a hannun ba” ta Gwamnan CBN, Godwin Emefiele.
Ya bayyana dagewar da Gwamnan Babban Bankin na CBN ya yi a ranar 10 ga watan Fabrairu na canjin Naira da kayyade fitar da kudade a matsayin rashin dacewa.