Wasu maza guda biyu sun sha mamaki bayan bayan gano cewa su biyu ne iyayen yarinya daya bayan duk sun je daukar yarinyar a wata makaranta da take aiki, Legit.ng ta ruwaito.
Mazan duk ‘yan kasar Amurka ne kuma kamar yadda wata ma’abociya amfani da TikTok mai suna @Sheena_20200 ta bayyana tare da wallafa bidiyonsu duk daga Georgia suke.
Sun je makarantar ne musamman don daukar yarinyarsu wacce ma’aikaciya ce mai babban mukami a makarantar, kuma ko wannensu yana tunanin diyarsa ce tsawon shekaru.
Yayin da su ka hadu, ko wannensu ya kalli dan’uwansa yana mai mamaki tare da tambayar juna akan cewa ya aka yi hakan? Daya cewa yayi:
“Wanene kai? Me kake nufi? Ni fa mahaifinta ne,” kamar yadda Sheena Jackson ta bayyana a bidiyon da ta saki.
Nan da nan wasu ma’abota amfani da kafafen sada zumuntar zamani na Amurka da ke da masaniya akan lamarin su ka fara bayyana yadda abin ya faru dalla-dalla.
An samu rahotanni akan yadda shugaban hukumar makarantar ya kira mahaifiyarta musamman don ta amsa tambayoyi kuma ta raba hatsaniyar.
Saidai a lokacin da ta bayyana ta fara ihu ne tana rusa kuka yayin da ko wanne cikin mazajen ya fara yunkurin lallasa dan’uwansa.
Yayin da taje makarantar, ta yi mamaki inda ta hau tambayoyi. Kai! Me ke faruwa? Meyasa ba ku fada min cewa za ku zo ba? a cewar Sheena.
Daga nan ne su ka koma filin da ko wannensu ya ajiye motarsa don su sasanta. Daya daga cikinsu ya fara dukanta a wurin, kamar yadda wani ma’aboci amfani da TikTok ya shaida.
An gano cewa matar ta dinga yaudarar mazan ne tana amshe kudadensu da sunan diyarsu ce su biyu. Daga bisani dai a caji ofis aka sakaya daya daga cikin mazan.
Saidai kakar yarinyar taje daukar ta don ko wannensu bai samu damar tafiya da ita ba don an yi kare jini biri jini.
Daga bisani wani rahoto ke nuna cewa babbar kawar matar ce take da alhakin tattaro mazajen don su san halin da ake ciki akan yadda dukansu ke daukar yarinya daya a matsayin diyarsu.
Da Yawan Ɗalibai Mata Sun Yi Ciki, Maza Kuma Sun Koma Kanikanci Inji NANS
Kungiyar dalibai ta kasa NANS, ta caccaki gwamnatin tarayya kan yajin aikin watanni bakwai da kungiyar malaman jami’o’i, ASUU ta shiga.
NANS ta ce yajin aikin na barazana ga ‘yancin dan Adam na daliban Najeriya, dangane da samun damar karatu.
Comrade Olusesi Tolulope Samson, shugaban NANS na Legas ne ya bayyana hakan a shirin safe na Arise TV a ranar Talata yayin da yake gabatar da tambayoyi kan zanga-zangar daliban a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas a ranar Litinin.
Ya ce yajin aikin ya shafi makomar mambobinsu, inda ya ce wasu dalibai maza sun zama makanikai; yayin da wasu dalibai mata suka samu ciki.
Ya yi nuni da cewa zanga-zangar da aka gudanar a filin jirgin ne domin a fadakar da kasashen duniya cewa wani abu ya tabarbare a Najeriya dangane da ilimi.
Shugaban daliban ya ce bukatar tasu ita ce a bude jami’o’in, inda ya ce daliban sun ci gaba da yin katsalandan a kan abin da zai kasance sakamakon ganawar da shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, da shugabannin kungiyar za su yi. ASUU.