Rundunar ‘yan sanda ta saki hotunan wasu bindigogu da harsasai da suka kwato daga hannun‘ yan bindiga a jihar Kaduna.
Kaduna na daya daga cikin jihohin da ‘yan ta’adda ke addabar mazauna garin.
ASP Muhamed Jalinge, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Kaduna shi ne ya fitar da hotunan, ya kuma ce, an kashe wani dan bindiga a yayin musayar wuta da jami’an’ yan sanda.
Jalinge ya kara da cewa, an saki wasu wadanda Yan bindigan suka yi garkuwa da su, daga Maboyar Yan bindigan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tinubu ya Iso Nigeria daga Burtaniya
Kazalika ya kuma fitar da hotunan wadanda ake zargi da fashi da makami da kuma Garkuwa da mutane, Wanda ya hada da wani jami’in dan sanda da yayi sojan gona.