Hukumar Shari’a ta Jihar Bauchi ta jagoranci lalatawa tsre da kona giya sama da kwali 500 biyar a Karamar hukumar Misau ta Jihar Bauchi.
A ranar Larabar da ta gabata ne dai Shugaban Hukumar Mustapha Baba Ilelah ya jagoranci wannan gagarumin aiki inda ta ce hakan wani mataki ne na kawar da miyagun ayyuka a Jihar matsayinta na Jiha mai yawan musulmi.
Wakilin Mu a Bauchi Bashir Khalid Furyam ya ruwaito mana cewa a dai ranar ta Laraba ne, hukumar shari’ar ta kaddamar da jami’an hukumar Hisbah a karamar hukumar a shirin da ake yi na kyautata ayyuka tsakanin al’umma.
Shugaban Hisbah a karamar hukumar Misau Abubakar Darazo ya bayyana cewa bisa irin bayanai ne da suka tattaro ne ya basu damar samun nasarar kama kwalaben giyar da adadin su ya zarta dubu biyar