Gidauniyar Fasahar Noma ta Afirka ta sanar da nadin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a matsayin jakadan Afirka kan fasahar noma.
Babban Daraktan AATF, Dr Canisius Kanangire ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Juma’a a Abuja bayan wata ganawa da tsohon shugaban kasar a Yenagoa dake jihar Bayelsa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kwana Ɗaya Kafin Biki, Kayan Ango Sun Ɓace, An Sace Sadaki A Wurin Ɗaura Aure a Kano
A matsayin jakadan AATF, Jonathan zai ba da shawarar ci gaban burin noma na Afirka da ci gaban tattalin arziki ta hanyar amfani da sabbin fasahohi da ingantacciyar saka hannun jari a aikin gona.
Jonathan, wanda ya rike shugabancin Najeriya daga shekarar 2010 zuwa 2015, an ce shi ne kan gaba wajen inganta noma a nahiyar.
Yayin da yake karbar nadin, ya ce a matsayinsa na tsohon shugaban kasa, sha’awar hidimar nahiyar ta samo asali ne sakamakon sha’awar samar da abinci da kuma kawo sauyi don samun ingantacciyar rayuwa a Afirka.
Babban Darakta na AATF ya bayyana cewa, aniyar Jonathan ta daukaka harkar noma a Nahiyar ta samu ajandar kawo sauyi a harkar noma da ya bi tare da aiwatar da shi sosai a Najeriya a lokacin da yake shugaban kasa.
Ajandar ta yi niyya ne don haɓaka aiki da riba a cikin zaɓaɓɓun kayan amfanin gona kusan 12, waɗanda suka haɗa da: auduga, koko, rogo, dabino, mai, masara, waken soya, albasa, shinkafa, kiwo, kifi, tumatur da dawa.
Kanangire ya ce a karkashin ajandar, an samar da sabbin guraben ayyukan yi kimanin miliyan 3.5 bisa wasu muhimman kayayyakin da aka zabo, yayin da aka samar da guraben ayyukan yi da dama daga wasu ayyukan sarkakkiya, inda sama da Naira biliyan 300 ake samun karin kudin shiga a hannun manoman Najeriya da ‘yan kasuwa na karkara.
Bugu da kari, an zuba sama da Naira biliyan 60 (dalar Amurka miliyan 380) a cikin tattalin arzikin kasar daga maye gurbin kashi 20% na garin biredi da garin rogo.
A cewar sanarwar, wani muhimmin abin da Jonathan ya bar noma a matsayinsa na shugaban Najeriya shi ne yadda ya iya rage shigo da abinci da za a iya nomawa a cikin gida, ta yadda zai ceto al’ummar kasar sama da Naira tiriliyan 1.3 a duk shekara wajen shigo da kayan abinci.
“Dr Jonathan ya iya nunawa a Najeriya cewa ya kamata a dauki aikin noma a matsayin kasuwanci kuma a tallafa wa manufofin da suka dace don inganta rayuwar al’ummarmu da ke noma,” in ji Kanangire.
Ya bayyana Jonathan a matsayin dan Afirka mai kishin kasa wanda ya tsaya tsayin daka wajen ganin an kawar da talauci a yankunan karkara da kuma zaman lafiya a nahiyar, don haka ya sa hannu wajen warware rikici cikin lumana a nahiyar.
Ya kara da cewa “AATF na da matukar farin ciki da samun tsohon shugaban kasar a matsayin jakadan mu, wanda aikinsa zai kara habaka kokarin da ake yi na inganta fannin noma,” in ji shi.
A wani labarin kuma, Gwamna Fintiri Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Mutane Uku Da Suka Mutu A Hatsarin Ayarin Motocinsa
Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa a ranar Alhamis ya yi ta’aziyyar rasuwar mutane uku da suka mutu a hatsarin mota kirar Toyota Hilux Van wanda take jigilar wasu ‘yan banga da ke cikin tawagar yakin neman zabensa zuwa yankin Gella Mubi ta Kudu da ke jihar.
Fintiri, a lokacin da yake zantawa da magoya bayansa a garin Gella dake yankin Mubi ta Kudu, ya ce ya damu matuka, kuma ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar PDP a wajen taron da su yi shiru na minti daya ga wadanda suka rasu.
“Jam’iyyar tana jimamin mutuwar mutane uku da ke cikin tawagar kuma suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota,” in ji Fintiri.