An nada Sarki Charles III a hukumance a matsyain sarkin a Austireliya da New Zealand a yau lahadi, , a bukukuwan bikin hawansa karagar mulki. Kamar yadda Punch ta ruwaito
A Canberra, Gwamna-Janar David Hurley ya yi shelar “Yarima Charles Philip Arthur George ya zama Sarki Charles III, da kuma , Sarkin Austiraliya”.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutum 3, Tare Da Lalata Gidaje Sama Da 1, 000 A Bauchi
A wani bikin makamancin haka a Wellington, Firaminista Jacinda Ardern ya yaba wa Charles, yana mai cewa “ya dade yana kaunar New Zealand, ya nuna matukar kulawar sa ga kasarmu”.
Bikin biyun sun kasance tagwayen juna kamar yadda tsare tsaren masarautar ta nuna.
A baya Dukansu ƙasashen wani bangare ne a Burtaniya, kuma sun kasance masu cin gashin kansu tsawon shekaru da yawa amma suna amfani da sarki a matsayin shugaban ƙasa.
Firaministan Australia, Anthony Albanese, wanda zai tafi Landan a wannan makon don halartar jana’izar Sarauniya Elizabeth, ya ba da sanarwar cewa ranar 22 ga Satumba za ta kasance ranar hutu a Australia don tunawa da mutuwar Sarauniyar.
A WANI LABARIN KUMA: Mun Baiwa Yan Kasashen Waje Sama Da 200 Shedar Zama Yan Najeriya—– Gwamnarin Tarayya
Gwamnatin tarayya ta sanar da baiwa wasu ‘yan kasashen waje dari biyu da tamanin da shida (286) takardar shaidar zama dan kasa da suka fito daga kasashe arba’in da tara.
Daily Post ta ruwaito cewa, Babban sakatare na ma’aikatar harkokin cikin gida, Dr Shuaib Belgore, ne ya bayyana hakan a cikin wata talla da ya sanyawa hannu kuma aka bai wa manema labarai a ranar Asabar.