Napoli ta gaya wa Manchester City ta biya ta Yuro miliyan 65 domin siyan dan wasan Senegal, Kalidou Koulibaly, wanda yake yana da shekaru 29 a duniya kamar yadda Daily Monitor suka tabbatar. Rahoton ya kara da cewa; ana kuma rade-radin cewa zai koma Liverpool ko Manchester United.
A wani labarin kuma Manchester City tana son siyan dan wasan Inter Milan dan kasar Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 22, domin maye gurbin Sergio Aguero, mai shekara 32 a shirinta na tsawon lokaci kamar yadda Sky Sports ta labarto.
Sai dai a wani rahoton kuma an ce Martinez yana dab da kammala yarjejeniya da Barcelona.