gubana

An Rantsar Da Sabon Gwamnan Jihar Yobe, Alh. Mai Mala Buni, Da Mataimakin Sa Alh. Idi Barde Gubana

Wakilinmu Mohammed Gambo Yobe

Bukin rantsar war ya gudana ne a sabon dakin taro dake gidan gwamnatin jahar Yobe, a birnin Damaturu.

A jawabin sa jim kadan bayan ya karbi karagar mulkin, Gwamna Mai Mala Buni yayi alkawura da dama ga ‘yan jahar Yobe.

Na farko, yayi alkawarin biyan sabon albashi ga ma’aikata Naira dubu 30, sa’annan ya saka dokar ta baci bangaren ilimi.

Daga bisani ya nemi goyon baya daga al’ummar jahar domin sauke nauyi dake kansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *