Rahotanni da suke fitowa daga jihar Kogi shi ne an rantsar da Edward Onoja, a matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar Kogi bayan da majalisar jihar ta tumbuke Simon Achuba wato tsohon mataimakin gwamnan bisa wadansu zarge-zarge.
Edward Onoja, kafin rantsar da shi shi ne shugaban shugaban ma’aikatan gwamnati, sannan shi ne mataimaki ga dan takarar gwamnan jihar Kogi a jam’iyyar APC wato Yahaya Bello a zaben da zai gudana a ranar 16 ga watan Nuwamban shekararnan.
An rantsar da Edward Onoja a yau Litinin a gidan gwamnatin jihar.