Hukumomin dake kula da tashoshin jiragen saman Nijeriya sun sanar da rufe daya daga cikin hanyoyin da jirage ke sauka a tashar Murtala Muhammed dake Lagos sakamakon matsalar da jirgin Azman ya samu daren yau.
Manajan hulda da jama’a na Hukumar Henriatta Yakubu ta sanar da cewar jirgin Azman mai lamba ZQ2325 ya samu matsala lokacin sauka da misalin karfe 7 na daren yau, inda tayar sa guda ta fashe, amma kuma babu fasinja ko matukin da ya samu rauni.
Jami’ar tace jami’an hukumar kula da tashohin jiragen da na hukumar kashe gobara da na Binciken hadaruka na can suna kokarin kawar da jirgin daga inda ya sauka.