Bayan sace daliban Sakandiren Gwamnati ta Kankara har 333 a jihar Katsina da ‘yan bindiga suka yi wanda daga bisani kungiyar Boko Haram ta yi ikirarin hannu a ciki, gwamnonin jihohi biyar sun rufe makarantun dake kafatanin jihohin baki daya sakamakon matsalar tsaro da kuma yaduwar cutar korona.
Kwamishinan Lafiya na jihar Zamfara Ibrahim Gusau ya ce matakin kulle makarantun 10 da ke iyakar jihar da Katsina da kuma wadanda ke Iyaka da Kaduna na da nasaba da sake tabarbarewar al’amuran tsaro.
Ibrahim Gusau ya bayyana cewa makarantun da ke tsakiyar gari za su ci gaba da tafiyar da al’amuransu kamar yadda su ke.
Gidan rediyon Faransa ya labarto cewa; tun bayan matakin sace daliban Sakandiren a Katsina ranar 11 ga watan nan da muke ciki, hankula suka fara tashi kan makomar ilimi musamman a makarantun kwana, inda tun a wancan lokaci gwamnatin Katsina ta yi umarnin kulle ilahirin makarantun kwana.
Zuwa yanzu dai babu tabbacin ko kulle makarantun a jihohin Kano da Jigawa na da nasaba tsaro musamman la’akari da tsanantar cutar korona wadda zuwa yanzu aka samu sabbin kamuwa mutum 14 a Jigawa.
Tun cikin daren jiya Talata ne gwamnatin Kanon ta bakin kwamishinan Ilimi na jihar Sanusi Kiru ya bayyana bukatar gaggauta kulle makarantun yayin da ya umarci iyaye yaran da ke makarantu kwana su gaggauta kwashe yaransu a yau Laraba.
Itama dai sanarwar kulle makarantun Jigawa ta bakin mukaddashin babban Sakataren ma’aikatar ilmi Rabi’u Adamu ta umarci iyaye su gaggauta kwashe yaransu daga makarantun kwana a yau Larabab baya ga umartar makarantun jeka ka dawo su ci gaba da kasancewa a kulle.
Haka zalika, a jihar Kaduna, tuni ma’aikatar ilimi ta bada umurnin kulle kafatanin makarantun dake jihar a wani mataki na dakile barazanar yaduwar cutar korona. Wanda dokar kulle makarantun zai fara aiki daga yau Laraba.
Kusan watanni 3 ke nan da makarantun suka sake budewa a sassan Najeriya musamman arewacin kasar wadanda aka kulle su saboda tsanantar korona, duk da cewa hada-hadar bukukuwa, kasuwanni da kuma tarukan siyasa na ci gaba da gudana kamar yadda aka saba.