An rufe Makarantun Firamare a Abuja saboda rashin albashi
Malaman Firamare dake Karamar hukumar Bwari a Abuja sun dukufa yajin aiki ana saura kwana biyu da jarabawa kan rashin biyansu albashin watan Yuni.
Malaman makarantun dai sun sallami yaran zuwa gidan su day safiyar ranar Laraba.
KARANTA:-An yakewa Habiba Abubakar shekaru bakwai gidan Kaso
Wani Malami dake Kubwa ya gana da Jaridar Dailytrust inda yace an bada sanarwar fara yajin akin ne a ranar Talata.
Wani kuma malamin cewa yayi makatantu shida dake yankin FCE duk an biyasu ta Bwari ne kawai ba’a biya ba.
Yace duk yunkurin da hukumar NUT tayi don ganin an baiwa Malaman albashin su sunyi amma hakan baisa an basu ba.