Shugaban kasar Tunisiya Kais Saïed ya rusa dukkannin majalisar dokokin kasar, wacce ya dakatar da ita watanni takwas da suka gabata, biyo bayan barkewar zanga-zangar a kasar.
Hakan ya biyo bayan wani taro da ‘yan majalisar suka yi ta yanar gizo a ranar Laraba inda suka kada kuri’ar soke dokar shugaban kasar da ta ba shi damar cigaba da rike madafun iko tun a bara.
Shugaban na Tunisiya ya kira matakin majalisar a matsayin “yunkurin juyin mulki”.
Ya ce majalisar ta “rasa halaccinta” kuma ta ci amanar kasar kana za a gurfanar da ‘yan majalisar da ke da hannu a wannan yunkurin a gaban kuliya.
Mr Saied ya dakatar da yan majalissar ne Kuma ya cigaba da rike Madadin Ikon kasar, Wanda hakan ya bashi damar sake rubuta kundin tsarin mulkin kasar. Bayan wannan mataki da ya dauka.
Tun bayan hakan ne, Zanga-Zanga ta barke a titunan kasar sakamakon durkushewar tattalin arzikin Tunisiya, Wanda kuma hakan ya kawo yamutsi tsakanin masu boren da yan sandan kasar.