Junaidu Danjuma daya daga cikin ɗiyan Mai riƙe da Sarauta a Gwombe na Masarautar Kuje dake Abuja Mai Martaba Danjuma Maji Jangaba, masu garkuwa da mutane sun sace shi.
Wakilin Majiyar mu ya ruwaito cewar wanda ke dauke da Ɗan Basaraken Kabiru Sani sun harbe shi, a lokacin da yake ƙoƙarin guduwa.
Jaridar Daily Trust ta bada rahoton cewa ƴan ƙauye 11 ciki har da matar Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP Mohammed Koriya, suma an sace su a yankin a farkon watan nan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar ‘Yan Sanda Ta Dakatar Da Jami’anta 2 Da Suka Yi Aiki A Karkashin DCP Abba Kyari
Wani Mazaunin Gwombe da ake kira da Salihu yace lamarin ya faru da misalin ƙarfe 5:23 a lokacin da masu garkuwa da mutanen suka ɗauki manyan bindigu inda suka bi kan hanyar Gwargwada-Gwombe.
Ya bayyana cewar ɗan Basaraken yana dawo wa ne daga Ƙauyen Rubochi a saman Mashin, a lokacin da masu garkuwa da mutane suka bayyana akan hanyar su.
“A lokacin da ya ga masu garkuwa da mutanen, wanda ke dauke da Ɗan Basaraken yayi ƙoƙarin guduwa, wanda ya sanya suka buɗe masu wuta, tare da kashe shi nan take, gami da tafiya da Ɗan Basaraken,” inji shi.
Sarkin Gwargwada-Ugbada Mai Martaba Alhaji Hussein Agabi Mam ya Tabbatar da sace ɗan Shugaban Kauyen Gwombe a tattaunawa dashi a waya.
Mai Magana da Yawun da Rundunar Ƴan sanda na Abuja DSP Adeh Josephine bai ɗauki waya ba, ko maido da saƙon karta kwana da aka tura mashi akan satar.