An dauke Jarirai lokacin da Yan bindiga suka afka wani Asibitin dake Zaria
Jaridar Dailytrust ta ruwaito cewar Mutane biyar aka dauke ciki harda Mata.
Yan bindigan, sun afka ciki asibitin adadi mai yawa, inda sukai batakashi da Yan sandan kusa da Asibitin.
KARANTA:-Jirgin Saman Sojin Kasar Philippines ya hallaka mutane 45
Daya daga cikin ma’aikatan asibitin wanda bai bari a ambaci sunan sa ba, ya shaidawa Jaridar Dailytrust cewar Yan bindigan sunyita harbe-harbe zuwansu asibitin.
Ya kuma ce babban masu gadin asibitin nada cikin wadanda akai garkuwa dasu.
Gaba dayan wadanda aka dauka Malaman asibitin mazauna gidajen dake cikin asibitinne, kawo yanzu dai mutane goma ne akai garkuwa dasu.
Mai kula da harkokin jama’a na asibitin Maryam Abdulrazaq tace akwai sunayen mutane shida daga cikin wadanda akai garkuwa dasu.
Tace wannan shine karo na shida da ake daukar ma’aikatan asibitin.
Lokacin da mai rahotanmu yaje wajan Yan sanda yace akwai alamun harsashi a katangar su.
An ce Yan ta’addan sun rufe hanyar dake zuwa daga Zaria lokacin da suke ta’adancin.
Lokacin da aka tuntubi shugaban Yan sanda na Jahar Kaduna Muhammed Jalinge ya tabbatar da aukuwar lamarin, yace ana Shirin zuwa kwato Mutanen da akai garkuwa da su.