By Abbas Yakubu Yaura
Mazauna garin Dakwa dake yankin karamar hukumar Tafa a jihar Neja har yanzu basu farfaɗo ba daga firgicin sace wani jariri ɗan wata huɗu a yankin ba.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Samhat Kabiru, an ce an sace tane daga hannun babban yayarta, wanda ta dauke ta daga harabar gidan su zuwa waje dake kusa da Layin-Hausawa, a cikin garin.
Mahaifiyar jaririyar, Fatima Kabiru, tace jaririyar tana bayanta ne a lokacin da take wanke tufafi, da misalin karfe tara na safe a ranar data dace, sai ta lura cewa jaririn bai gamsu da yanayin ba.
“Don haka na dora ta a bayan yayarta mai shekara biyar. Amma ko ta yaya, yarinyar ta fita da jaririn, Da na gane haka, sai na fita nemanta – na duba gidaje biyu na makwabta amma ban gansu ba.
“Daga baya na gano ta a wani titi kusa da inda nake tana kururuwar neman agaji, da ganina sai ta kara fashe da kuka, tana cewa mummy wani ne ya kwace mana jariri daga baya na, ya zagaya ta wannan lungun.
“Mun garzaya zuwa wajen amma ba mu iya gano mutumin ba,” Fatima ta kara da cewa.
Mahaifiyar ta ci gaba da cewa, an kai rahoton lamarin ga ofishin ‘yan sanda dake unguwar, inda ta kara da cewa, kawo yanzu babu wani ci gaba mai kyau.
A halin da ake ciki, ko da mazauna yankin ba su farfaɗo da lamarin ba, an dakile wani yunkurin sace wata yarinya mai shekaru 12 a ranar Juma’ar da ta gabata.
Yarinyar mai suna Maryam Umar, yayin da take bayyana wa manema labarai abin daya faru da ita a kofar gidansu dake Unguwar Kamba da misalin karfe biyu na rana.
Tace “Mutumin yana zaune a cikin mota, sai yaga na fito daga gidanmu, sai ya garzaya zuwa gare ni,da zuwan sa ya zuba mini wani abu, wanda hakan ya sa na ji rauni da zafi a idanuna. Sannan kuma ya gargadeni kancewa zai soka min wuka idan kikayi Ihu ko wani abu makancin haka duk da haka, na yi tsayin daka yayin da yake jani zuwa ga abin hawansa. Na yi ta fama sai da na zame daga rikon shi, ” a cewar Maryam.
Wata mai gidan abinci a yankin Asiya Nuhu da aka ganta tare da yarinyar a yayin wannan hirar tace Maryam ta kasance tana taimaka mata wajen gudanar da wasu kananan ayyuka a wurin.
Da yake tsokaci, Sarkin Hausawa na Dakwa, Alhaji Aliyu Shehu, yace an samu irin wannan matsalar ta barayin kananan yara a yankin, amma abin da ya faru a baya-bayan nan ya fi ban mamaki da rashin mutuntaka.