Wakiliyarmu Maryam Musa Kaduna
Mutanen Garin Udawa da ke Karamar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna, sun koka Mutuka da Yadda Barayin Shanu ke cin Karen su Babu Babbaka a Kauyen Unguwar Dan Maliki da Sauran Kauyakun da ke Zagaye da Garin na Udawa.
A lokacin da Wakiliyarmu ke Zantawa da wani daga cikin Mazauna Kauyen Mai Suna Hon. Sagir B Udawa, cewa Yayi Tun Shekaran Jiya Barayin Shanu ke Kwashe mana Dukiya har yau din nan da nake Magana da ku.
Ya cigaba da cewa Akalla Cikin Kwanaki Ukun nan Sun Sace Mana Shanu Sama da Dubu Biyar Dan haka ma wasu daga Cikin mu suka Nemo Motar Tirela, domin Kwashe Shsnun su Zuwa tudun mun Tsira.
Wanda yanzu haka mun yi Tirela ta fi Goma a nan Wurin Kamar yadda kuke Gani da Idon Ku Saboda mu tsira da rayuwarmu da dukiyoyin mu.
Duk Kokarin da muka yi na Samun Kakakin Rundunar ‘yan Sandan Jihar Kaduna, abin ya ci Tura.