Gwamnatin jihar Fulato ta sanya dokar ta kaita zirga-zirga na awa 24 a karamar hukumar Jos ta Arewa , biyo bayan Kara samun tashin hanka sanadiyar harin da aka kai kauyen Yelwa Zangam dake karamar hukumar, inda aka kashe sama da mutane 35, da kuma lalata kadarorin milliyiyon nairori.
A cewar Gwamnan jihar Lalong dokar zata fara aiki ne da musalin karfe 4 na yammacin yau Laraba, 25 ga watan Agustan shekarar 2021, har zuwa fitowar wata sanarwar.
Ya Kara da cewa, ya zama wajibi a dauki wannan matakin, biyo bayan barazanar asarar rayuka da dukiyoyin a karamar hukumar, domin kauce wa Saba wa doka da oda.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutane 8 sun mutu a wani sabon hari a Benue
Kazalika ya ce, dokar ta awa 24 za ta taimakawa hukumomin tsaro, wajan tabbatar da zaman lafiya, da kuma yunkurin su, na zakulo Maharan da suka kaiwa kauyen hari.
Gwamna Lalong ya kuma ja kunnen al’umar karamar hukumar Jos ta Arewa, da su kasan ce masu biyayya ga wannan doka ta awa 24 da zata fara aiki a yau.
Har’ilayau gwaman ya ce, dokar 6 na yamma zuwa 6 na safe a karamar hukumar Jos ta Kudu, da karamar hukumar Bassa nanan daram.