By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta cafke wani mutum mai suna Oliver Jamker daga Ughelli, jihar Delta bisa zargin yin garkuwa dashi.
Rundunar ‘yan sandan a cikin wata sanarwa da ta fitar dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Bello Kantongos, tare da rabawa manema labarai a Benin, ta ce wanda ake zargin ya tsere daga gidan gyaran hali na Oko a lokacin zanga-zangar kawo karshen #EndSARS ta shekarar 2020.
Ya kara da cewa, rundunar ‘yan sanda ta Ugbowo karkashin jagorancin jami’in ‘yan sanda reshen jihar, Albert Udeme, ta samu labarin yadda wasu ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da mutane hudu da mutanensu suka kai dauki tare da kubutar da wadanda abin ya shafa a gidan yarin.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A ranar 29/12/2021 da misalin karfe 14:30 na rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta bangaren Ugbowo karkashin jagorancin jami’in dan sanda Albert Udeme ya samu labarin cewa wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da Kelvin Omonedo ‘M’, Adeleke Wasiu ‘M’ a titin Olienhen kuma suka wuce zuwa hanyar ukhumwem a cikin garin Benin, inda suka kuma yi garkuwa da wasu mata ‘yan biyun Irene Edenabuohen ‘F’ da Rosemary Ojegue ‘F’.
“Bayan samun labarin, sai jami’an ‘yan sanda na sashen suka fara kai farmaki, suka bi sawun ‘yan ta’addan tare da harbin bindiga, karfin wuta na tawagar ‘yan sandan ya sa ‘yan bindigar suka yi watsi da wadanda abin ya shafa suka kama daya daga cikin wadanda abin ya shafa. Wadanda ake zargin sun bayyana sunan sa da Oliver Jamker ‘M’ na Ughelli, jihar Delta kuma dan gudun hijira daga gidan gyaran halin na Oko a lokacin zanga-zangar #EndSARS na shekarar 2020. Ana ci gaba da kokarin kama ‘yan kungiyar da suka gudu.”