By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Filato tace an sake kama fursunoni bakwai da suka tsere daga gidan yarin Jos bayan da ‘yan bindiga suka kai hari a yammacin ranar Lahadi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Ubah Ogaba wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa daya fitar ranar Lahadi da daddare, yace, “A ranar 11/28/2021 da misalin karfe 5:20 na yamma,wasu ‘yan bindigar da ba a san ko su wanene ba suka kai hari a cibiyar gidan gyaran halin ta Jos, ina wasu fursunonin suka tsere.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “Bayan samun rahoton, kwamishinan ‘yan sandan jihar Filato, CP Bartholomew N. Onyeka, wanda ya jagoranci tawagarsa zuwa wurin, ya bayar da umarnin a killace cibiyar baki daya.
Sannan ya ci gaba da cewa, “CP ya kuma bayar da umarnin dakatar da bincike cikin gaggawa inda ‘yan sanda suka sake kama wasu mutane bakwai da suka tsere kuma suna tsare yayin da wani daya tsere ya mika kansa ga ‘yan sanda bisa radin kansa.
“Bisa amsa kiran gaggawar da aka yi, an shawo kan lamarin da taimakon manyan bindigogin Jami’an tsaro.
“CP ya sake tabbatar da cewa a halin yanzu ‘yan sanda da sauran Hukumomin tsaro suna nan a kasa don hana ‘yan baranda ta’addancin da suke son aikatawa na munanan ayyukan su. A halin da ake ciki, ana kan shawo kan lamarin.”