An sake kama wani Kurma da kai da Hannun Mutum a Rivers
Wani ɗan shekara 23 kurma, an kama shi da Kan Mutum da hannaye, wanda jami’ar tsaron zaman lafiya da shawara wato ONELGA, dake Jahar Rivers Suka yi.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Kakabawa Mali Takunkumi Ba Tare Da Son Rai Ba, Shugaban Ivory Coast, Ouattara
Majiyar mu tace wanda ake zargin Chinedu Okoro an kama shi a ranar Asabar 15 ga watan Janairu, bayan an same shi da kan wata tsohuwa da hannu a jakar shi a Omoku ta Jahar Rivers.
Wanda ake zargin wanda aka kama tuni an miƙa shi ga Ƴan sanda domin gudanar da bincike.