Wasu ‘yan bindiga a Afrika ta Kudu sun sake kashe wani dan Nijeriya mai suna Chikamso Ufordi.
Chikamso Ufordi dan asalin Karamar Hukumar Awgu da ke Jihar Inugu ne. ‘Yan bindigan sun kai masa hari tare da wasu mutum biyu da misalin karfe 7 na yammacin ranar Asabar a Nigel ta Afrika ta Kudu.
Kakakin ‘yan Nijeriya Mazauna Afrika ta Kudu, Odefa Ikele ne ya tabbatarwa da Kamfanin Dillacin Labaran Nijeriya da afkuwar lamarin.
Shi dai garin Nigel wani dan karamin gari ne da ke yankin Gauteng kusa da Birnin Johannesburg.