Wasu sabbin dalibai 13 daga garin Chibok, wadanda suka kammala wani shiri a karkashin makarantar New Foundation na daga cikin wadanda suka yi rantsuwar a jami’ar Amurka dake Najeriya.
Sun bi sahun wasu sabbin dalibai daga dukkan jihohi 36 na Najeriya, Ruwanda, Jamhuriyar Nijar da Kamaru, don halartar taron Rantsar da Dalibai na zangon shekarar 2022 tare da iyaye, abokai da dangi.
A cikin wata sanarwa a jiya, Babban Daraktan Sadarwa na Jami’ar, Daniel Okereke, ya ce daliban Chibok sun shiga shirin ne kan tallafin karatu na Gwamnatin Tarayya.
“A karkashin kulawar Ma’aikatar Mata ta Tarayya, Jami’ar AUN ta horar da su a cikin hazikan mata, masu son sanin ya kamata, kuma masu kishin kasa wadanda ke shirye don amfanan rayuwarsu, jami’a da sana’o’in da suka koya, bayan kammala karatunsu,” in ji shi.