Girgizar kasa mai karfin maki 6.4 ta afku a kudancin kasar Turkiya.
Ta afku ne makonni bayan da wata mummunar girgizar kasa ta yi barna a yankin wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 46,000. Daily Post ta ruwaito.
KU KARANTA: Dalilin Maye Gurbin Naja’atu Muhammad Da Wani, Yan Awanni Da Sanar Da Naɗin ta
A cewar wata majiyar gwamnati, ta bakin hukumar takaita annoba da taimakon gaggawa, Afad ta ce girgizar ta afku a yankin da misalin karfe 20:00 na safe agogon kasar.
Magajin garin Hatay da ke kudancin Turkiyya ya ce mutane sun makale a karkashin baraguzan gine-gine.
Girgizar kasa mai karfin awo 7.8 ta afku a wannan yanki a ranar 6 ga Fabrairu, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 46,000.
Hukumomin Turkiyya sun sami afkuwar girgizar kasa sama da 6,000 tun bayan girgizar kasar da ta afku a yankin kuma ta ce girgizar ta yau (Litinin) ta fi karfi fiye da ta baya.
Ga mutanen dake yankin, da iftila’in ya faru a baya, har yanzu basu gama farfadowa ba daga irin asarar da suka tafka.
A wani labarin kuma: Sauya Fasalin Naira: Gwamnonin APC 3 Sun Gana Da Ministan Shari’a
Gwamnonin jam’iyyar APC guda uku a ranar Litinin din nan sun gana da ministan shari’a, Abubakar Malami da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, kan manufar musanya Naira.
Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa taron ya dauki kusan awa daya ana gudanar da shi a sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa a ranar Litinin din nan.