Gwamnatin jihar Filato ta sake sassauta dokar hana fita a Jos ta Arewa, tare dage dokar hana zirga-zirgar keke-Napep a yankin.
Wata sanarwa da Darektan yada labaran gwamnan jihar Dr. Makut Simon Macham ya fitar, ta ce, daga yanzu, dokar hana fitar za ta fara aiki daga 10 na dare zuwa 6 na safe.
“Gwamna Simon Lalong, ya amince dokar ta fara aiki ranar Laraba 8 ga watan Satumba 2021.” Sanarwar ta ce.
KARANTA WANNAN LABARIN: An kama wani Mai shekara 64 da yi wa Yar shekara 2 fyade
Hukumomin jihar sun ce an dauki wannan mataki ne bayan wani taro da majalisar tsaron jihar ta yi a jiya Talata 7 ga watan Satumba shekarar nan, inda aka duba yanayin tsaro a birnin na Jos.
A karshen watan Agusta aka saka dokar hana fita har tsawon sa’a 24, daga baya aka sassauta ta koma 6 na yamma zuwa 6 na safe.
Saka dokar ta biyo bayan rikici da birnin Jos ke fuskanta a yan kwanakin nan, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, tare da asarar dukiyoyi.
“Kazalika, daga ranar Laraba 8 ga watan satumba 2021, an dage dokar hana zirga-zirgar keke-napep, inda yanzu za su rika aiki daga 6 na safe, zuwa 6 na yamma.” Sanarwar ta kara da cewa.
Gwamna Lalong ya kuma yi kira ga al’umar jihar da su ci gaba da ba gwamnatin hadin kai, wajen ganin an tabbatar da zaman lafiya a fadin jihar.