Hukumar rubuta jarabawar shiga manyan makarantu wato JAMB, ta sanar da sakamakon Jarabawar JAMB ɗin na wannan shekara.
Jarabawar dai ta gudana ne yan kwanakin nan, kuma tuni ba tare da wata-wata ba hukumar ta saki sakamakon.
Kakakin Hukumar ta JAMB Mista Fabian Benjamin shi ya sanar da sakin sakamakon a wata sanarwa a ranar Juma’a.
Fabian Benjamin ya ce lashakka hukumar ta ji daɗi matuka bisa jarabawar ta gudana ba tare da wata tangarda ba, kuma a cewarsa nasarar hakan ta biyo bayan amfani da lambar shaidar dan kasa ta NIN ne.
To sai dai kawo yanzu akwai sakamakon wasu ɗalibai da ba a sake ba, biyo bayan bincike da ake ci gaba da gudanarwa, kamar yadda hukumar ta bayyana.