Yan bindiga da suka yi awon gaba da shugaban kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah a Jihar Kogi sun sake shi.
Da yake jawabi wa manema labarai a birnin Lokaja fadar gwamnatin Jihar Kogi, Sakataren ƙungiyar Adamu Abubakar ya shaida cewa tun daren shekaran jiya mutanen suka saki shugaban nasu a birnin tarayya Abuja.
Adamu ya ce bisa irin bayanan da shugaban nasu yayi bayan sako shi, sun gano cewa wadanda suka yi awon gaba da shi ba ma masu garkuwa da mutane ba ne kamar yadda aka yi hasashe, hasali ma ana ganin kamar jami’an tsaro ne.
Ya kara da cewa tuni kuma Damina ya hade da iyalan shi dake Chikara na Jihar ta Kogi.
Tun da farko da ma a ranar 4 ga watan Mayu ne Sakataren Ƙungiyar ya shaida wa manema labarai cewa, wasu cikin kayan sarki sun je gidan shugaban nasu wuraren karfe takwas na dare inda suka yi awon gaba da shi.
Duk da cewa ana lokaci ne na zama kamar yadda sakataren kungiyar ya shaida amma duk wasu yunkuri da suka yi na ji daga Shugaban nasu al’amarin ya faskara domin duk wayoyinsa ba sa shiga.