Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta tabbatar da sakin mutane 4 daga cikin fasinjojin da aka yi garkuwa da su a kan titin Emohua/Kalabari na hanyar da ta hada yankin Gabas da Yammacin jihar a ranar Asabar din da ta gabata. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Grace-Iringe-Koko, wadda ta bayyana hakan a Fatakwal a ranar Talata, ta ce an sako mutanen ne a daren ranar Litinin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ambaliyar Ruwa Ta Mamaye Gidaje 400 A Jihar Filato
Kakakin ‘yan sandan, ya yi kira ga wadanda abin ya shafa da su kai kan su ga shalkwatar rundunar ‘yan sandan jihar domin baiwa ‘yan sanda damar samun saukin sako sauran wadanda lamarin ya shafa da har yanzu suke hannun su.
Ta tabbatar wa masu amfani da hanyar cewa “an tura taqagar ‘yan sanda” zuwa yankin don kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
SP Iringe-Koko ta kuma yi kira ga shugabannin kananan hukumomi hudu da ke kewayen titin Emohua Kalabri da su hada kai da jami’an tsaro domin a samu saukin kamawa tare da hukunta masu garkuwa da mutane da suka addabi yankin.
Sai dai ba a bayyana ko an biya wani kudin fansa don sako mutanen da aka sacen ba.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa an yi garkuwa da fasinjoji biyar na wata motar kasuwanci a ranar Asabar da misalin karfe 8 na dare a kan hanyar Emohua, Kalabari
A WANI LABARIN KUMA: Har Yanzu Buhari Bai Cika Ko Daya Daga Cikin Alkawuran Da Yayi Ba – Tsohon Kakakin PDP
Tsohon Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP na Kasa, Kola Ologbondiyan, ya ce alkawuran da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi, bai cika su ba
Ologbondiyan, wanda ya yi magana a cikin wani shiri na gidan talabijin Channels TV Mai suna “Sunrise Daily” ya ce abin dariya ne a yi maganar inganta tattalin arzikin Najeriya a karkashin wannan gwamnati