An sako wani limamin Darikar Katolika da wasu suka yi garkuwa da shi cikin makon jiya a yankin renon Ingila na kasar Kamaru.
Rahotanni sun ce; shugabannin darikar na yankin Mamfe ne suka tabbatar da sakin Monsignor Julius Agbortoko, bayan kwanakin uku da ya yi a hannun wadanda suka sace shi.
Mutanen da suka kame limamin na Katholikan na Kamaru, sun bukaci da a ba su CFA miliyan 20 kafin su sake shi.
Yammacin kasar Kamarun dai na fama da rikicin ‘yan aware da yanzu ya shiga shekaru hudu, inda sama da mutum dubu uku da 500 suka mutu wasu sama da dubu 700 kuwa suka tsere wa gidajensu.