By Abbas Yakubu Yaura
Masu garkuwa da mutanen sun sako shugaban kungiyar makarantu masu zaman kansu na kasa reshen jihar Delta, Monday Ifoghere, tare da matarsa, bayan sun kwashe kwanaki bakwai suna tsare a hannunsu.
Rahotanni sun bayyana cewa an saki mata da mijin ne da misalin karfe 5 na safe a kewayen Eku axis a karamar hukumar Ethiope ta Gabas a ranar Lahadi.
Jaridar PUNCH ta tattaro cewa an yi zargin cewa iyalan sun biya Naira miliyan 12 a matsayin kudin fansa, tare da gudunmawar abokan hulda da masu hannu da shuni.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa kwanaki bayan sun yi awon gaba dasu da karfin tsiya, masu garkuwan sun bukaci kudin fansa naira miliyan 200, sannan suka mayar da shi zuwa naira miliyan 100 daga karshe kuma ya koma naira miliyan 12.
An dai sace Deacon Ifoghere da matarsa ne a ranar Lahadi, 12 ga watan Disamba, 2021, a kusa da kasuwar Okro dake Egbo, Kokori a karamar hukumar Ethiope ta Gabas a jihar Delta yayin da suke dawowa daga taron da suka halatta na dangin su zuwa Ughelli.
Wakilinmu ya tattaro cewa tuni wadanda lamarin ya rutsa dasu nacan kwance a asibiti kuma suna karbar magani a wani asibiti da ba a bayyana ba.
Mataimakin shugaban NAPPS na kasa na shiyyar (Kudu maso Kudu), Dokta Ochuko Akpeme, yayin da yake tabbatar da sakin mijin da matar ya shaidawa manema labarai cewa labarin ya kara masa karfin gwiwa kamar yadda ya nuna godiya ga Allah.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda reshen jihar Delta, Bright Edafe, ba’a samu jin ta bakinsa kan lamarin har zuwa lokacin hada wannan rahoto.