An sallami Maryam Katagun daga Asibitin
Ministan kamfanoni, kasuwanci da habbaka hannun jari, Maryam Katagun, ta yanke jiki ta fadi a wani taron gaddamar da tallafi a Bauchi ranar Litinin data gabata.
An sallami Maryam Katagun a ranar Talata, sannan aka tafi da ita zuwa Abuja.
KARANTA:-Yan sanda Sun kubutar da Mai bai wa Gwamnan Cross Rivers Shawara
Idan baku manta ba mun kawo maku cewar, a wancan satin Maryam Katagun ta yanke jiki ta fadi lokacin da take kaddamar da wani tallafi a Bauchi.
Nan take aka kaita asibitin Abubakar Tafawa Balewa aka kwantar da ita.
Likitocin dake kula da ita sun ce, “Ministan ta yi ayyuka wanda suka haifar Mata da gajiya shi ya kawo hakan.”
An dai sallami Ministan misalin karfe tara sannan aka maida ta Abuja.