An sake gano wasu gawarwakin maza biyu a wani bene mai hawa 21 da ya ruguje a Ikoyi da ke Legas.
Hakan ya biyo bayan da Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya bayyana mutuwar mutane 42 a safiyar ranar Asabar, wanda hakan ya kara adadin wadanda suka mutu daga 42 zuwa 44 tare da 15 da suka tsira.
A halin da ake ciki, gwamnatin tarayya ta umurci rundunar Injiniya ta Sojoji da su taimaka wajen aikin ceto.
Shugaban rundunar Injiniya Birgediya Janar Omali, ya isa wurin a jiya, inda hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA, da kwamishinonin ayyuka na musamman da tsare-tsare na jihar Legas suka tarbe su.
Janar Omali ya ce tawagar sojojin tana wurin ne bisa umarnin daga babban Birnin Tarayya Abuja.
Tun da farko, Gwamna Sanwo-Olu ya bayyana shirin gwamnatin jihar na bayar da tallafi ga wadanda ginin ya rufta.
Ya ce, “Ba ma bukatar sanar da jama’a batun karfafawa, amma muna son tabbatar da cewa muna hulda da mutanen da suka dace,” ya kara da cewa ana gudanar da ayyukan jin kai da zamantakewa ga wadanda suka tsira.