Rahotanni sun bayyana cewar ana ci gaba da samun rahotanni yadda jinsin Mata suka afka dabi’ar shaye shaye gadan gadan a Najeriya.
Har ila yau masu binciken sun bayyana cewar Matan sun shagaltu da shan ko wane nau’in kayan maye ciki harda Koken.
Bayanin hakan na kunshe cikin wata zungureriyar takardar bayanai da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyin wato NDLEA, reshen jiyar Ribas, ta fitar a ranar yaki da shan miyagun kwayoyi ta duniya na wannan shekarar.
Shugaban hukumar reshen Jihar Ribas din, Mista Rachael Shelling, shiya bayyana hakan ya ce sun kama a kalla kwayoyi masu nauyin Kilo giram Dubu goma shekarar data gabata.
Ya ce su a nasu tunanin Yan kwayoyi da Tabar Wiwi kawai zasu yi karo da su a lokacin da suke kai samame abun mamaki kawai sai suka tarar da Manyan kayan maye masu tsadar gaske ciki harda Hodar koken, kuma Mata sun fi tsunduma cikin harkar; inji shi.