By Abbas Yakubu Yaura
Rahotonnni sun bayyana cewa an samu tashin gobara a tsohuwar harabar Jami’ar Bayero dake kabuga bayan Babban Masallacin dake cikin jami’ar ta jihar kano.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Hukumar kashe gobara ta jihar kano ta bayyana cewa lamarin ya faru da misalin karfe 2:45 na dare yayin da wani mai suna Sa’idu S Abubakar ya kirasu inda suka isa wajen da misalin karfe 2:52 na dare dan bada taimakon daya dace.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar kano, Saminu Yusuf Abdullahi shine wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin sanarwar da ya rabawa manema labarai a kano
“Inda ya bayyana cewa an sami a sarar a sakamakon tashin gobarar inda dakin taro guda daya da dakin karatu guda biyu da dakin ajiya shima guda daya dukkanin su sun kone, sai dakin gwaje-gwaje guda daya dake saman beni shima rabinsa ya kone”,a cewar sa.
Kazalika Yusuf ya kara da cewa mu sabbabin faruwar wannan hatsari wutar lantarki ce ta haddasa inda ta bazu zuwa sauran sassan makarantar, kuma yace aikin ceton ya gudana tsakanin su da jami’an hukumar kashe gobara ta jami’ar inda suka kashe wutar.